Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Yadda Kuda Yake Tashi da Kuma Juyawa

Yadda Kuda Yake Tashi da Kuma Juyawa

 Duk wanda ya taba kokarin kama kuda ya san cewa yin hakan na da wuya sosai. Kamar walkiya, kwarin nan sukan kauce wa duk wani kokarin kama su.

 ’Yan kimiyya sun gano cewa kudan da ke bin ’ya’yan itatuwa zai iya tashi da kuma juyawa yadda jiragen yaki suke yi, kuma zai iya yin hakan sau da yawa cikin sakan daya. Wani farfesa mai suna Michael Dickinson ya ce: “Da zarar an haifi kuda suna iya tashiwa kamar gwanaye. Yana kamar a ce ka saka jariri cikin jirgin sama kuma ya iya tukawa.”

 Sa’ad da masu bincike suka dauki hoton kudan nan yayinda yake tashi, sun gano cewa kudan yana kada fikafikansa sau ɗari biyu cikin sakan daya. Amma kuma idan ya kada fikafikansa sau daya kawai, kudan za ya iya fahimtar yanayin da yake ciki kuma ya dauki matakin kauce ma hadari nan take.

 Yaya yawan lokacin da kudan yake bukata don ya dauki matakin kauce wa hadari? Masu bincike sun gano cewa kudan tana iya yin hakan sau 50 da kiftar ido. Dickinson da aka ambata dazu ya bayyana cewa: Kudan yakan yi wani lissafi mai wuya cikin dan kankanin lokaci don ya gano inda hadari yake da kuma yadda zai tsere ma hadarin.

 Yadda dan karamin kwakwalwar kuda yake yin wadannan abubuwan abin ban mamaki ne ga ’yan fasaha da masu bincike suke kokarin su fahimta.

Kuda yakan kauce domin ya guji wa hadari kuma zai iya yin hakan sau da yawa a cikin sakan daya

 Mene ra’ayinka? Yadda kuda yake tashi da kuma juyawa sakamakon juyin halitta ce? Ko akwai wanda ya halicce shi?