Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Karfin Sansanawa na Kare

Karfin Sansanawa na Kare

 Masu bincike sun ce kare na iya yin amfani da hancinsa don ya san shekaru da jinsi da kuma yanayi da wasu karnuka ke ciki. Kari ga haka, ana iya horar da karnuka don su san inda akwai bama-bamai ko kuma mugayen kwayoyi. ʼYan Adam na yawan yin amfani da idanunsu don sanin abin da ke faruwa kewaye da su, amma karnuka suna yin amfani da hancinsu. Kamar dai suna yin kome da hancinsu ne.

 Ka yi la’akari da wannan: Karfin sansanawa da kare ke da shi ya fi na ’yan Adam sau dubu. A binciken da aka yi a makarantar National Institute of Standards and Technology da ke Amirka, an ce kare yana iya sansana ya gane kamshi, kome kankantarsa. An kwatanta hakan da mutumin da ya zuba kwatar sukari daga karamin cokali cikin ruwan tafkin filin wasan Olimfik kuma ya dandana ruwan don ya ji zakin sukarin.

 Me ya sa karfin sansanawa na kare ya fi na ’yan Adam?

  •   Hancin kare yana a jike, shi ya sa yake saurin kama kamshi.

  •   Kare yana da rami biyu a hancinsa. Yana numfashi da daya kuma yana sansanawa da dayan. Idan kare ya sansana abu, iska tana shigowa gefen hancinsa da ke kama kamshi.

  •   Girman sashen hancin kare da ke sansana abu ya kai santimita dari da talatin ko fiye da hakan, amma na ’yan Adam santimita biyar ne kawai.

  •   Kare yana da abu a hancinsa da ke kama kamshi da ya fi na ’yan Adam sau hamsin.

 Duk wadannan abubuwan ne suke sa kare yake bambanta kamshi. Alal misali, wasu gwanaye sun ce za mu iya sansana miya mu san ko wace iri ce, amma kare zai iya gane kamshin dukan kayan miya da aka dafa miyar da ita.

 Masu bincike a Pine Street Foundation, wato makarantar binciken ciwon kansa sun ce kwakwalwar kare da hancinsa suna aiki tare kuma babu wata na’ura a duniya da ta kai hakan jin kamshi. Masana kimiyya suna kera hanci mai amfani da lantarki domin su iya gane wurin da aka ajiye bama-bamai da haramtattun kayayyaki da kuma cututtuka, har da ciwon kansa.

 Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa yadda kare yake sansana abu sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?