Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Abin da Ya Sa Lemun Pomelo Ba Ya Fashewa

Abin da Ya Sa Lemun Pomelo Ba Ya Fashewa

 Pomelo wani babban lemu ne mai zaki da ke girma a kan itace. Ko da lemun ya fado daga itace mai tsawon kafa 30, ba ya fashewa! Me ya sa wannan lemun ba ya fashewa?

 Alal misali: Masana kimiyya sun gano cewa akwai wani abu mai kama da soso tsakanin lemun da bawonsa. Abin da ke kama da soson yana girma kuma yana dauke da iska ko kuma ruwa. Idan lemun ya fado, soson yana hana shi fashewa, sai jikin ya yi tauri maimakon ya fashe.

 Masana kimiyya suna gwada katifar karfe da suka kera da yadda aka tsara jikin lemun pomelo. Sun gaskata cewa suna iya kera hular kwano na babur da abubuwan da za su kāre motoci da kuma tashar jirgin da ke zuwa duniyar wata da yadda aka tsara jikin lemun pomelo.

 Mene ne ra’ayinka? Kana ganin abin da ke sa lemun pomelo ba ya fashewa sa’ad da ya fado sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?