Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Yadda Dolfin Ke Sanin Zurfin Ruwa

Yadda Dolfin Ke Sanin Zurfin Ruwa

 Kifin Dolfin takan yi kara da fito iri-iri. Bayan haka, sai ta saurara ta ji wurin da karar ta kai don ta soma tafiya zuwa wasu wurare a mahallinta. Abin da ke taimaka wa dabbar ta yi hakan shi ne bakinta mai tsini. Saboda haka, masanan kimiyya suna kera na’urar jin kara a cikin ruwa don su magance matsaloli da ke tattare da na’urar da suke amfani da shi a yanzu.

 Alal misali: Wannan abu da ke taimaka mata da ake kira sonar yana sa ta gano kifin da ke boye a cikin kasa a teku. Kari ga haka, yana taimaka mata ta san bambanci tsakanin kifi da dutse. Wani farfesa mai suna Keith Brown da ke Jami’ar Heriot-Watt a birnin Edinburgh a kasar Scotland, ya ce: ‘Tun daga nisan kafa 32 da digo 8, wannan kifin zai iya sanin bambanci tsakanin durom da ke dauke da ruwan sha da ruwan gishiri da ruwan lemu da kuma mān fetur.’ Masanan kimiyya za su so su kera na’urori da za su iya yin irin wadannan abubuwan.

Tun daga nisan mita goma, dabbar dolfin za ta iya sanin abin da ke cikin durom

 Masu bincike sun duba abin da ke sa dabbar dolfin yin kara da jin kara, kuma suna kokarin kwaikwayon sa. Hakan ya sa sun kera wata na’ura da aka saka cikin silinda da ke da tsawon kafa 3 da digo 3. An kera wannan na’urar da aka hada a jikin ’yar tsana mai kama da mota don ta rika bincika kasar teku. Kari ga haka, za ta nemo abubuwa da aka binne a kasa kamar su kebura ko bututun māi kuma ta yi hakan ba tare da taba su ba. Wadanda suka kera wannan na’urar sun ga cewa za a iya amfani da ita a masana’antun mān fetur da kuma gas. Na’urar za ta inganta yadda ake samun bayanai kuma za ta taimaka wa injiniyoyi su saka na’ura a karkashin ruwa a wurin da ya fi kyau don su gano abubuwan da suka lalace a injin hakar māi. Ban da haka, zai taimaka musu su binciko abubuwan da suka toshe bututun.

 Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa yadda dolfin ke sanin zurfin ruwa sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?